in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'in MDD ya jaddada muhimman shirya zaben shugaban kasa a Mali
2018-01-24 12:31:44 cri
Mataimakin babban sakataren MDD wanda ke kula da shirin wanzar da zaman lafiya Jean-Pierre Lacroix, ya bukaci a samar da wani yanayi wanda zai bada damar shirya zaben shugaban kasar Mali.

Lacroix, ya fadawa taron kwamitin tsaron MDD cewa, zaben shugaban kasar a Mali zai kafa wani sabon shafi a shirin wanzar da zaman lafiya a kasar.

Yace akwai bukatar a samar da wani muhimmin yanayi na shirya zaben da kuma aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiyar kasar.

Lacroix, yace amincewar da aka yi na fitar da jadawalin zaben kasar a makon jiya, wani muhimmin mataki ne na yarjejeniyar wanzar da zaman lafiyar kasar.

A cewarsa, jadawalin zabukan kasar ya kunshi dukkan matakai da za'a yi amfani dasu wadada zasu kawo cigaba a harkokin shugabanci, da sha'anin tsaro, gabanin gudanar da zaben shugaban kasar a tsakiyar watan Yuli, inda ya bukaci gwamnati da sauran bangarori masu ruwa da tsaki dasu mutunta jadawalin zabukan kasar.

Lacroix yayi gargadin cewa, lokaci yana kurewa kuma kasar Mali tana cigaba da fuskantar karuwar matsalolin tsaro da tabarbarewar yanayin 'yancin dan adam da matsanancin yanayin jin kan al'umma. Masu aikin ceto sun ce, kimanin sama da 'yan kasar ta Mali miliyan 4.1 wato kwatankwacin kashi 22 bisa 100 na yawan al'ummar kasar ne zasu iya fuskantar matsalar kasancin abinci a wannan shekara 2018.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China