Jami'in harkokin kasuwanci a sashin hadin gwiwa a ma'aikatar harkokin kasuwancin kasar Sin Han Yong ya yi bayani cewa, a wannan karo, an bullo da ka'idojin sa ido kan harkokin zuba jari a kasashen waje, wadanda suka hada da gudanar da binciken shirin da kuma fanninsa, tattara bayanan shirye-shirye tare, da kuma hukunta wadanda suka sabawa ka'idoji.
Haka kuma, ana gudanar da bincike kan dukkan harkokin zuba jari, da suka hada da sha'anin kudi da wanda bai shafi sha'anin kudi ba.
Alkaluman kididdigar na nuna cewa a shekarar 2017, yawan kasashe da yankuna da kasar Sin take zuba jari kai tsaye ya kai 174, inda aka zuba jari dallar Amurka biliyan 120.08, adadin da ya ragu da kashi 29.4 bisa dari bisa na shekarar 2016. Kuma wannan shi ne karo na farko da adadin ya ragu tun daga shekarar 2003 da aka fara gabatar da shirin. (Maryam)