Ma'aikatar ciniki da zuba jari ta kasar Sin, ta ce yankin tsakiyar kasar Sin na kokarin zama wata cibiyar dake jan hankalin masu zuba jari na kasashen waje.
Mataimakin shugaban ma'aikatar ciniki da zuba jari ta kasar Sin Wang Shouwen, ya ce ba kamar yankunan gabar ruwa dake gabashin kasar ba, yankin tsakiyar kasar na da wasu damarmaki dake jan hankalin masu zuba jari na kasashen ketare, wanda ya kara mizanin awon harkokin zuba jarin waje na kai tsaye a kasar cikin watani ukun farkon shekarar nan.
Wang Shouwen ya bayyana haka ne yayin wani taron manema labarai kan taron bajakoli na yankin tsakiyar kasar Sin na 2017, wanda zai gudana a Hefei, babban birnin lardin Anhui tsakanin ranakun 17 da 19 ga watan Mayu.
Lardunan tsakiyar kasar Sin guda shida, sun hada da Anhui da Henan da Hubei da Hunan da Jiangxi da kuma Shanxi.
Masu fitar da kayyayaki na kasar Sin na iya fitar da kayayyaki ta jirgin kasa zuwa tsakiyar Asiya da Turai, yayin da kayayyakin da ake sarrafa a tsakiyar kasar ka iya mamaye kasuwannin gabashi da yammacin kasar.
Lardunan tsakiya na kasar Sin na samar da guraben aikin yi, inda mutane daga yankunan gabar ruwa ke kaura zuwa yankunan na tsakiya domin neman aiki ko kafa kasuwanci.(Fa'iza Mustapha)