Kaza lika rahoton ya bayyana cewa, bisa alkaluman kididdiga, kaso kusan 90 bisa dari na irin wadannan kamfanoni masu zaman kansu ne, kuma sun shafi fannoni daban daban, ciki hadda na samar da jari, da sabbin sana'o'i, da samar da jami'ai kwararru ga nahiyar.
A daya hannun rahoton ya bayyana sassa 5 da suka kunshi cinikayya, da zuba jari da samar da kayayyakin more rayuwa, da na ba da tallafi, a matsayin wadanda kasar ta Sin ta fi sauran kasashe tasiri a nahiyar ta Afirka.
Bugu da kari rahoton ya gano cewa, dangantaka tsakanin Sin da nahiyar Afirka ta kara bunkasa cikin shekaru 10 da suka gabata, inda harkokin cinikayya tsakanin sassan suke ci gaba, da kaso kusan 20 bisa dari a duk shekara, kana sashen zuba jari kai tsaye ke fadada, da kaso 40 bisa dari a kowace shekara.
Rahoton ya ma ce kudaden da 'yan kasuwa Sinawa ke shigarwa Afirka na iya haura hasashen da ake yi da kaso 15 bisa dari, idan aka hada da sauran sassa da ba a kididdige su ba. (Saminu Hassan)