in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Asusun zuba jari na kasar Sin ya zuba jarin dala biliyan 4.4 a nahiyar Afrika
2017-06-15 09:58:00 cri
Asusun raya nahiyar Afrika ta kasar Sin CAD, wanda bankin raya kasashe ta kasar Sin ke kula da shi, ya zuba jarin da ya kai dala biliyan 4.4 a kan ayyuka 90 a Afrika.

Yayin wani taro a birnin Harbin dake arewa maso gabashin kasar Sin, mataimakin shugaban asusun na CAD Wang Yong, ya ce ya zuwa karshen watan Mayu, an zuba jari a kasashen Afrika 36 a fannonin da suka hada da masana'antu da ababen more rayuwa da sauransu.

Gwamnatin kasar Sin ce ta kafa asusun sama da shekaru 10 da suka gabata, domin samar da hanyoyin da za su saukakawa kasar zuba jari a Afrika, inda a gundarin jarin asusun ya kai dala biliyan 10.

Wang ya ce asusun dake aiki bisa ka'idojin kasuwanci, ya yi nasarar hada kamfanonin kasar Sin da ayyuka da dama a nahiyar Afrika cikin sama da shekaru 10 da suka gabata.

A cewar Wang Yong, har yanzu kasashen Afrika na fuskantar kalubalen karancin jari da rashin ingantattun kayayyakin more rayuwa, inda ya ce kawancen kasar Sin da Afrika na da dimbin dammamaki da kuma kyakkyawar makoma.

A nasa bangaren, Jakadan Tanzania a Kasar Sin Mbelwa Kairuki, ya ce, kawancen na Afrika da Sin, harka ce ta morar juna, kuma asusun na CAD ya taka muhimmiyar rawa. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China