Baya ga kasar Holland, sauran kasahen biyar na da wa'adin aiki na tsawon shekaru biyu, wato daga farkon bana zuwa karshen shekara ta 2019. Ita kuwa kasar Holland, bisa yarjejeniyar da ta cimma da kasar Italiya, wa'adin aikinta zai kare a karshen shekarar da muke ciki, wato ranar 31 ga watan Disamban bana.
A halin yanzu, akwai kasashe membobi kwamitin sulhun 15, ciki har da kasar Sin da Faransa da Rasha da Birtaniya da Amurka, wadanda suka zama membobin dindindin, yayin da sauran kasashe goma suke matsayin membobin da ba na dindindin ba.
Ana zabar kasashe don zama membobin kwamitin sulhu na MDD da ba na dindindin ba, daga manyan nahiyoyi biyar na fadin duniya, inda tsawon shekaru biyu ke kasancewa wa'adin aikinsu.(Murtala Zhang)