AU ta nuna fargabar ne a lokacin wani muhimmin taron da ta gudanar karo na 11 wanda cibiyar nazari game da ayyukan ta'addanci ta Afrika (ACSRT), ta shirya a ranar Lahadi a birnin Algiers na kasar Algeriya.
Kungiyar AU ta bayyana damuwa inda ta ce dawowar mayakan zuwa Afrika zai iya gurgunta yunkurin tabbatar da zaman lafiya da tsaron nahiyar, kasancewar mayakan za su iya kafa wasu sabbin kungiyoyin ta'addanci wadanda za su yi amfani da su wajen kaddamar da hare haren ta'addanci, ba kawai a yankunan dake fama da matsalar tsaro ba, har ma da yankunan da ba su taba fuskantar barazanar hare haren ta'addancin ba.
Kimanin mayakan Afrika dubu 6 ne suka shiga kungiyar IS mai fafutukar kafa daular musulunci a kasashen Iraki da Syria, wadanda ake tsammanin za su iya komawa gida bayan da aka yi galaba kan kungiyar ta IS. Smail Chergui, jami'in wanzar da zaman lafiya da tsaro na kungiyar AU, ya ruwaito wani rahoton MDD cewa, wajibi ne kasashen Afrika su hada kansu don su yi aiki tare don magance barazanar tsaron.(Ahmad Fagam)