in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumar kare muhalli ta MDD za ta kafa cibiyar hadin gwiwar muhalli a tsakanin Sin da Afirka
2017-12-06 13:30:56 cri
Jiya Talata, hukumar kare muhalli ta MDD ta fidda rahoton cewa, za ta hada gwiwa da kasashen Sin da Kenya domin kafa cibiyar kula da harkokin muhalli a tsakanin Sin da Afirka, domin karfafa musayar fasahohin kare muhalli tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka.

A yau ne, za a kammala babban taron muhalli na MDD karo na 3 da aka shirya a birnin Nairobi, fadar mulkin kasa ta Kenya. An shirya taron ne domin karfafa hadin gwiwar dake tsaknain gwamnatoci, kamfanoni da al'ummomin kasa da kasa a fannin magance matsalolin gurbata muhalli. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China