in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU ta bukaci a kara dabarun tabbatar da tsaron sashen kula da lafiyar al'umma a nahiyar
2018-01-19 10:49:32 cri
A ranar Alhamis majalisar tsaro da zaman lafiya ta kungiyar tarayyar Afrika (AU) ta shirya tattaunawa game da barazanar dake addabar sashen kula da lafiyar al'umma a nahiyar ta Afrika.

Majalisar ta amince zata yi hadin gwiwa da cibiyar rigakafin yaduwar cutuka ta Afrika wato (Africa CDC), domin kai dauki wajen yaki da barkewar annoba, da yaki da magungunan da suka saba da yanayin jikin al'umma, da kuma yaki da barazanar karuwar yaduwar kwayoyin cutukan da basu yaduwa ta hanyar iska a nahiyar.

Da yake jawabi a lokacin taron, John Nkengasong, daraktan cibiyar ta Africa CDC, ya bukaci dukkan bangarori dasu bullo da dabaru da yin hadin gwiwa wajen yakar barazanar cutukan don bada kariya ga nahiyar.

Majalisar ta nuna bukatar karfafa ajandar kula da lafiyar alummar Afrika wanda ke kunshe cikin shirin samar da zaman lafiya da tsaro na AU.

Majalisar ta ayyana cewa barkewar annobar cutar Ebola ta yi matukar illa ga tattalin arzikin nahiyar, da haifar da barazana ga yanayin tsaro da walwalar jama'a a kasashen yammacin Afrika a yayin da aka tura dakarun sojoji su kula da tabbatar da tsaro da zaman lafiya.

Majalsiar ta kuma bayyana cewa Afrika tana fuskantar barazana game da yadda magungunan kashe kwayoyin cutuka suka saba da jikin jama'a lamarin dake haddasa mutuwar a kalla mutane miliyan 4.1 a duk shekara kana an yi hasashen samun hasarar dala tiriliyan 42 na tattalin arzikin na Afrika nan da shekarar 2050.

Afrika tana fuskantar kalubaloli daga wasu nau'ika na kwayoyin cutuka da basa yaduwa ta hanyar iska dake boye kamar cutar koda, da sankara, da cutar data shafi numfashi, da ciwon suga da dai sauransu.

Majalisar tace kamata yayi cibiyar Africa CDC ta yi aiki tare da dakarun sojin AU wajen zurfafa ayyukan zama cikin shirin ko-ta-kwana na yaki da kwayoyin cutuka, kuma su hada gwiwa wajen aikin bada horo game da kai dauki yayin barkewar cutuka, da samar da kayayyakin aiki da nufin karfafa sha'anin shirin kula da lafiya.

A watan Janairun 2017, kungiyar kasashen Afrika ta kaddamar da cibiyar rigakafin yaki da cutukan ta Africa CDC, da kuma yin hadin gwiwa da wasu cibiyoyi dake sassa biyar na kungiyar ta AU. (Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China