in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Batun yaki da rashawa ne ya kankane ajandar taron kolin AU, inji ministan wajen Habasha
2018-01-24 10:39:56 cri
Ministan harkokin wajen kasar Habasha ya bayyana cewa, batun yaki da ayyukan rashawa shine ya kasance jigon taron kolin kungiyar tarayyar Afrika karo na 30 dake gudana a Addis Ababa.

An bude taron na AU karo na 30 ne a ranar Litinin a helkwatar kungiyar tarayyar Afrikar, taken taron na wannan karo shine "Samun nasara a yaki da rashawa: Hanyar samun dawwamammen cigaba" taron kolin wanda ke gudana sau biyu a kowace shekara za'a kammala shi a ranar 29 ga watan nan na Janairu.

Da yake zanatawa da manema labarai, Workneh Gebeyehu, ministan harkokin wajen Habasha ya bayyana cewa, a halin yanzu, an dauki batun yaki da rashawa a matsayin wani muhimmin batu dake da nasaba da zaman lafiya da cigaban harkokin siyasar kasashen Afrika.

Yace ma'aunin ayyukan rashawa da yadda za'a yaki matsalar sune muhimman abubuwan da ake auna ingancin ma'aikatun gwamnati da kuma samun gwamnati mai tsabta a kowace kasa.

Gebeyehu ya kara da cewa, kasancewar daga cikin adadin al'ummar nahiyar Afrika kusan mutane biliyan guda, kaso 70 bisa 100 matasa ne, don haka yaki da ayyukan rashawa tamkar samar da kyakkyawar makoma ne ga mammobin kasashen na AU 55.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China