Ministan wanda ya bayyana haka Larabar nan yayin taron manema labarai, ya ce ana sa ran shugabannin za su tattauna kan batutuwan siyasa da tsaro da ke damun kasashen Afirka da kuma gyaran fuskan da ake fatan yiwa kungiyar da aka kafa shekaru 54 da suka gabata.
Taken taron kungiyar na wannan karo wanda aka bude a ranar Litinin, shi ne "Yaki da cin hanci da rashawa: hanya mai dorewa ta farfado da nahiyar Afirka". A ranar 29 ga wannnan wata ne ake fatan kammala taron, wanda aka saba gudanarwa sau biyu a shekara.
Kungiyar AU dai ta ayyana shekarar 2018, a matsayin shekarar yaki da cin hanci da rashawa a Afirka. (Ibrahim Yaya)