in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU ta yi tur da kalaman cin mutuncin da Trump ya furta
2018-01-17 10:20:20 cri
Majalisar raya tattalin arziki da zamantakewa da ala'du ta kungiyar tarayyar Afrika (ECOSOCC) ta fitar da sanarwa a jiya Talata, inda ta kalubalanci kalaman cin mutuncin da shugaban Amurka Donald Trump ya furta kan kasashe masu tasowa.

Majalisar ta ce ta yi matukar kaduwa game da samun labarin kalaman da Trump ya furta inda ya tozarta al'ummar Afrika da mutanen dake da tushen Afrika.

Majalisar ta ce wadannan kalamai sun yi matukar muni, kuma ba daidai ba ne shugaba irin na Amurka ya aikata haka, majalisar ta kara da cewa, a nahiyar Afrika ana matukar girmama dattijai kuma ana girmama kalaman da dattijai ke furtawa musamman irin kalaman da suka yi amfani da su wajen bayyana matsayarsu. Shugaban Amurka dattijo ne kuma wajibi ne a ko da yaushe ya rika mu'amala irin ta dattijai, in ji sanarwar.

Sanarwar ta ce ana girmama mutanen duniya ne bisa matsayinsu da kuma irin yadda suke mutunta kalaman dattaku da suke furtawa. Yin amfani da kalamai wajen nuna wariyar launin fata wani mataki ne da zai kara ruruta wutar rikici a duniya wanda ake samun yawaitar hakan a wasu sassan duniya.

Sanarwar ta ce sun bukaci shugaban na Amurka da ya gaggauta janye kalaman nasa, kuma ya nemi afuwar dukkan al'ummar Afrika da mutanen dake da tushen Afrika a duk fadin duniya. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China