Taron ya kuma samu halartar jakadun kasashe 55 na mambobin kungiyar dake Addis Ababa da kuma manyan jami'an kungiyar da sauransu.
A cewar shugaban, taken taron kolin kungiyar na wannan karo, shi ne, "yaki da cin hanci da rashawa: hanya mai dorewa ta farfado da nahiyar Afirka". Ana kuma sa ran taron wakilan na PRC zai duba tare da tattauna batutuwan da suka shafi aikin gona, sufuri, kimiya da fasahar kere-kere, watsa labarai da harkokin sadarwa na zamani da kuma batutuwan da suka shafi dokoki da harkokin kudi. (Ibrahim Yaya)