in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tattalin arzikin Sin ya kara bunkasa a shekarar 2017
2018-01-22 15:47:28 cri

Kakakin hukumar bunkasa ci gaba da gudanar da sauye sauye ta kasar Sin Yan Pengcheng, ya ce tattalin arzikin kasar ya bunkasa a shekarar 2017, yanayin dake cike da inganci, da kyautata, tare da tsari managarci.

Yan Pengcheng ya ce GDPn kasar na shekarar 2017 ya karu zuwa 6.9 bisa dari, wanda hakan ya nuna "babban tagomashi da aka samu".

Yan Pengcheng ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai, inda ya tabo wasu sassa na ci gaban tattalin arziki da tsare tsare da Sin ta samu a shekarar, ciki hadda bunkasar albarkatu, da ta kasuwanni, da ma fadadar tsare tsare dake tallafawa ci gaban tattalin arzikin kasar.

Ya ce, yayin da ake samun karin sauye sauye a kasar, dukkanin sassa na aiki tukuru wajen samar da abubuwa da ake bukata domin amfanin al'umma, da kara inganta tsarin samar da su.

Tuni dai alkaluman kididdigar kasar ta Sin na shekarar 2017, suka nuna cewa, a fannin kara inganta kayayyakin bukata, kasar ta samu ci gaba na kaso 6.6 bisa dari, wanda hakan ya sauya koma bayan da kasar ta samu a wannan fanni cikin shekaru 6 da suka gabata.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China