Mafi yawan bukatun neman buga tambarin masana'antu an gudanar da su ne ta shafukan intanet, tun bayan da kasar Sin ta zamanintar da tsarin buga tambarin masana'antun, kamar yadda hukumar gudanar da harkokin ciniki da masana'antu ta kasar Sin ta ayyana.
Ya zuwa karshen shekarar 2017, kasar Sin tana da cikakkun tamburan da kamfanonin suka yi rejista kimanin miliyan 14.92, wanda shi ne adadi mafi yawa a duk fadin duniya.
Sabbin manyan kamfanonin kasar Sin 37 sun shiga sahun fitattun kamfanoni mafiya girma na duniya 500 a shekarar da ta gabata, inda aka samu karin kashi 150 idan aka kwatanta da shekarar 2013, kamar yadda hukumar tantace tambarin masana'antu ta duniya ta bayyana.
Bugu da kari, kasar Sin ce kasa ta 3 mafi girma wajen mika bukatun neman yin rejistar kamfanoni a karkashin tsarin yin rijistar kamfanoni na duniya, inda take da bukatun yin rejistar kimanin 4,810 a shekarar 2017, sama da kashi 59.6 bisa 100 idan an kwatanta da na shekara shekara, hakan ya nuna yadda kamfanonin kasar Sin ke kara samun bunkasuwa a tsarin kasuwannin duniya. (Ahmad Fagam)




