in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta agazawa kungiyoyin tallafawa masu kananan karfi wajen rage talauci
2018-01-21 12:56:51 cri
Kasar Sin za ta ci gaba da tallafawa ayyukan kungiyoyin dake agazawa marasa galihu wajen ba su kwarin gwiwa don rage radadin talauci, mataimakin ministan kula da jin dadin al'umma Gao Xiaobing, shi ne ya bayyana hakan a jiya Asabar.

Gao, ya bayyana hakan a lokacin taron tallafawa al'ummar kasar Sin na shekara shekara.

Ya ce ma'aikatarsa ta bukaci hukumomin dake kula da walwalar jama'a da su kara azama wajen tallafawa mutanen dake fama da talauci a yankunansu ta hanyar bada taimako ga kungiyoyin dake agazawa marasa galihu.

Idan za'a iya tunawa, kasar Sin ta sha nanata aniyarta na samar da al'umma mai matsakaiciyar wadata kafin nan da shekarar 2020, wanda hakan zai tabbata ne ta hanyar kawar da radadin talauci.

Ya zuwa karshen shekarar 2016, akwai Sinawa kimanin miliyan 43.35 dake rayuwa kasa da ma'aunin tattalin arziki na yuan 2,300 kwatankwacin dala 344 a matsayin kudin shigarsu a shekara, adadin da ya kama kashi 3 bisa 100 na yawan al'ummar kasar Sin.

Domin cimma wannan burin nan da shekarar 2020, gwamanatin Sin tana fatar tsame mutane miliyan 10 daga kangin fatara a duk shekara, wato kimanin mutane miliyan guda ke nan a duk wata, ko kuma mutane 20 a duk cikin minti guda ake sa ran za su yi ban kwana daga kangin fatara. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China