in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan sanda Sinawa na aiki bisa hadin gwiwa da takwarorinsu na kasashen ketare wajen tabbatar da tsaro
2017-09-25 11:25:35 cri
Ma'aikatar kula da tsaron al'umma ta kasar Sin ta ce, jami'an 'yan sanda da aka girke a ofisoshin jakadancin da wakilci na kasar Sin, sun taimaka wajen kamawa da maido da sama da mutane 1,000 da ake zargi da aikata laifi zuwa kasar Sin a karshen 2016, a wani bangare na shirin hadin gwiwa da kasashen ketare kan inganta tabbatar da tsaro.

A cewar ma'aikatar, zuwa yanzu, kasar Sin ta tura jami'an 'yan sanda 64 zuwa kasashen 31.

Ta ce jami'an sun taimaka wajen yaki da laifuffuka 4,460 tsakanin kasa da kasa, kuma sun taimakawa 'yan sanda a kasar Sin bibbiyar jerin laifuffukan da aka aikata ta wayar tarho a kasashen Thailand da Philippines.

Jami'an sun kuma taka muhimmiyar rawa wajen kare rayuka da dukiyoyin Sinawa dake ketare. (Fa'iza Msutapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China