in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta sha alwashin taimakawa zaman lafiyar duniya inji ofishin jakadancin kasar dake Amurka
2017-12-19 20:01:59 cri
Mai magana da yawun ofishin jakadancin kasar Sin dake birnin Washington na kasar Amurka, ya ce kasar sa ta sha alwashin tallafawa dukkanin wasu matakai, wadanda za su kai ga wanzuwar zaman lafiya da lumana, tare da ci gaban duniya, da daidaito tsakanin kasa da kasa.

Kakakin ofishin jakadancin na Sin na wannan tsokaci ne bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana manufofin tsaron kasar sa a jiya Litinin. Cikin manufofin, shugaba Trump ya bayyana kasashen Sin da Rasha a matsayin abokan takara, kuma 'yan hamayyar kasar sa, wadanda ke kalubalantar manufofin Amurkar a dukkanin fannoni.

Game da hakan jami'in jakadancin na Sin ya ce, zaman lafiya da samar da ci gaba, su ne muhimman manufofin da duniya ta sanya gaba a halin yanzu. Ya ce duk wani yunkuri na kaucewa hakan zai zamo abun kyama, ba kuma zai kai ga cimma wata nasara ba.

Kaza lika ya ce daukar Sin a matsayin abokiyar adawar Amurka, ya sabawa manufar da Amurkar ta bayyana a baya, na daukar Sin a matsayin abokiyar hadin gwiwa.

Kaza lika ya kaucewa manufar sassan biyu na kasancewa masu dogaro da juna ta fuskar ci gaba, da aniyyar su ta fadada alaka a harkokin duniya.

Daga nan sai jami'in ya bayyana hadin kan Amurka da Sin, a matsayin abun da zai samar musu da moriya ta bai daya, yayin da kuma fito na fito zai haifarwa sassan biyu babbar hasara. Ya ce abu mafi dacewa shi ne Amurka ta fahimci yanayin ci gaban kasar Sin, ta kuma rungumi hakan, ko a kai ga samun wanzuwar yanayi na zaman lafiya.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China