in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta kaddamar da tsarin ko ta kwana na tsaron yanar gizo
2017-06-28 09:56:54 cri

A jiya Talata ne babban ofishin dake lura da harkokin da suka jibanci tsaron yanar gizo na kasar Sin, ya fidda wai sabon tsari mai kunshe da matakai daban daban, wadanda suka shafi ba da kariya ga yanar gizo a sassan kasar.

Matakan dai sun hada da na kandagarki, da dakile yawaitar barna, da ba da kariya ga bukatun jama'a, da tabbatar da tsaron kasa, tare da wanzar da doka da oda. Karkashin tsarin an raba fannonin tsaron yanar gizo gida shida, wadanda suka hada da lura da illar kutse wanda ke illa sannu a hankali, da matsalar dake bijirowa sakamakon wasu ayyuka na gudanarwa, da hari da a kan kai kan yanar gizo. Sauran sun hada da satar bayanai, da kuma kutse cikin sha'anin tsaron yanar gizon.

Kaza lika an raba matakan hadari da ake iya gamuwa da su a wannan fanni gida hudu, tsakanin mataki na gama gari zuwa mai matukar hadari. Misalin abubuwan da ka iya aukuwa, karkashin mataki mai matukar hadari akwai dakatar da muhimman ayyukan yanar gizo, ko haddasa rashi na bayanan tsaron kasa masu matukar amfani, wanda hakan ka iya zama babbar barazana ga tsaro da zamantakewar al'umma.

Har ila yau, bisa tsarin, matakan da ake iya dauka a irin wannan yanayi, sun kunshi kafa helkwatar gaggawa ta tsaro, da sanya ido tare da gudanar da ayyukan ko ta kwana na tsawon sa'o'i 24, domin kawo karshen matsalar da ta auku.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China