in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Manyan wakilan mambobin BRICS za su gana a Sin game da tsaro
2017-07-25 10:06:06 cri

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang ya bayyana cewa, taron mambobin kungiyar BRICS game da batun tsaro karo na 7 zai gudana a birnin Beijing daga ranar 27 zuwa 28 ga wannan wata na Yuli.

Lu, ya bayyana cewa, taron da ake shirin gudanarwa zai tabo batutuwa da suka hada da harkokin gudanar da mulki na kasa da kasa, da yaki da ta'addanci, da batun tsaron hanyoyin sadarwa na internet, da tsaron makamashi, da sauran batutuwa da suka shafi kasa da kasa da shiyya shiyya, har ma da batun tsaron kasa da ci gabanta.

Lu, yana fata taron zai kara kare muradun mambobin kasashen, da karfafa sha'anin siyasa da tsaro da kuma kara hadin kai tsakanin mambobin na BRICS, da karfafa manufofin kungiyar BRICS, kana taron zai taimaka wajen shirye shiryen gudanar da taron kolin na BRICS wanda za'a gudanar a birnin Xiamen na kasar Sin a watan Satumba.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China