in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen Sin, Pakistan, da Afghanistan za su tattauna batun karfafa dangantakar tattalin arziki
2017-12-27 11:30:29 cri
Ministocin kasashen wajen Sin, Pakistan da Afghanistan a ranar Talata sun amince za su tattauna game da hanyoyin da za su kara bunkasa dangantakar tattalin arziki karkashin shirin hadin gwiwa na kasashen uku wato (CPEC) a takaice.

Bisa la'akari da muhimmancin makwabtaka dake tsakanin kasar Sin da kasashen Pakistan da Afghanistan, kasashen sun nuna sha'awar kafa wani tsari da zai taimaka wajen gina ci gaban tattalin arziki da kyautata yanayin rayuwar al'ummomin kasashen, kuma matakin zai kara inganta yanayin cudanya tsakanin sassan dake yankin, in ji ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi.

Wang Yi ya ce, kyautata yanayin zaman rayuwar al'ummar dake zaune a iyakokin kasashen shi ne makasudin fadada wannan shiri. Ya kara da cewa bangarorin uku sun cimma matsaya za su kara zurfafa mu'amala karkashin shawarar nan ta "ziri daya da hanya daya".

Hadin gwiwar kasashen na CPEC, zai kunshi batun sada juna da manyan hanyoyin mota, da na Layin dogo, da bututan mai, da aikin jiragen ruwa karkashin shawarar "ziri daya da hanya daya", wanda a halin yanzu aikin ke gudana a Pakistan baki daya.

Hanyar mai tazarar kilomita 3,000 ta fara ne daga yankin Kashgar na kasar Sin inda ta kare zuwa Gwadar na kasar Pakistan, wanda ya hada da hanyar cinikin siliki da ake gudanarwa a arewaci da kuma na cinikin siliki ta kan teku a karni na 21 zuwa kudanci. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China