in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi ya ce kasar Sin a shirye take ta karfafa kyakkyawar mu'amala da Rasha a shekarar 2018
2017-12-31 18:50:04 cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana a yau Lahadi cewa, a shirye yake ya yi aiki da takwaransa na kasar Rasha Vladimir Putin, wajen yin hadin gwiwa don daga matsayin dangantakar dake tsakanin kasashen biyu daga dukkan fannoni.

Xi ya bayyana hakan ne a sakon taya murna na sabuwar shekara da ya aikewa Putin.

A cikin sakon, shugaba Xi a madadin gwamnatin Sin da al'ummar Sin, ya gabatar da sakon fatan alheri ga shugaba Putin na Rasha da al'ummar kasar ta Rasha.

Ya ce kasar Sin tana kokarin kyautata mu'amalarta da Rasha, kana za ta lalibo sabbin hanyoyin da za su kara karfafa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.

Ya kara da cewa, shekarun 2018 da 2019 za su kasance shekaru ne na kara karfafa hadin gwiwa da yin musaya tsakanin kasashen biyu, Xi ya ce wannan mataki zai kara tabbatar da kulla kyakkyawar dangantaka tsakanin kasar Sin da Rasha, kuma zai taimakawa tunanin bangarorin biyu wajen kara yin cudanya da abokantaka don ciyar da kasashen da ma al'ummominsu gaba.

A sakonsa na martani, Putin ya bayyana cewa, dangantakar dake tsakanin kasar Rasha da Sin a shekarar 2017 ta samu gagarumin ci gaba, kasancewar matsayin alakar cinikayya dake tsakanin kasashen biyu ya kai wani babban matsayi, kana an samu bunkasuwa a bangarorin ci gaban fasaha, da musayar raya al'adu a tsakanin al'ummomin kasashen biyu.

A wani labarin kuma, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya aike da sakon taya murnar sabuwar shekara ga takwaransa na Rasha Dmitry Medvedev a yau Lahadi, kuma dukkan manyan jami'an biyu sun yaba da irin ci gaba da aka samu ta fuskar karfin dangantaka tsakanin kasashen biyu. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China