Babban jami'i a ma'aikatar Lyu Yugang ya shaidawa manema labarai a jiya Alhamis cewa, duk da karuwar adadin daliban sakandare a kasar, yankunan dake fuskantar koma baya a tsakiya da yammacin kasar na ci gaba da fama da karancin kayayyakin koyo da koyarwa, sannan ci gaban fannin ilimin sana'o'i na tafiyar hawainiya.
Lyu Yugang ya kara da cewa, akwai rashin daidaito tsakanin sauran fannonin ilimin sakandare da kuma ilimin sana'o'i a gabashin kasar.
A cewar wani jadawali da ma'aikatar ta fitar jiya, daga shekarar 2017 zuwa 2020, kasar za ta inganta ilimin sana'o'i a makarantun sakandare da samar da kayayyakin koyo da koyarwa da kuma kara yawan kudin da ake warewa bangaren.
Jami'in ya ce, za a kara yawan kayayyakin aiki a makarantun dake yankunan dake fuskantar koma baya tare da tabbatar da hakkin ilimi ga dalibai masu bukata ta musammam da 'ya'yan da suka fito daga gidaje masu karamin karfi da na ma'aikata masu kaura. (Fa'iza Mustapha)