in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin: Ana fadada yawan makarantun share fagen shiga firamare
2017-05-17 10:08:33 cri

Gwamnatin kasar Sin, ta bayyana burin ta na fadada yawan makarantun share fagen shiga firamare, ya zuwa kaso 85 bisa dari na yaran da shekarun su, suka kai daf da shiga makarantun firamare nan da shekarar 2020, adadin da zai karu da kaso 10 bisa dari, idan an kwatanta da abun da kasar ke da shi a halin yanzu.

Wani kundi mai kunshe da tsarin kashi na uku, ya nuna cewa, samar da kyakkyawan yanayi na fadada karatun yara na share fagen shiga firamare da kaso 80 bisa dari nan da shekarar 2020, na da muhimmanci cikin burin bunkasa ilimi na kasar.

A shekarar 2010 dai Sin ta samar da dama ga kaso 50.9 bisa dari, na yaran kasar masu shiga karatun share fage, gabanin fara aiwatar da tsarin kashi na uku.

Sabon shirin dai na nufi gwamnati za ta samar da karin kudade na gudanarwa domin cimma nasarar shirin, ta yadda sassan masu zaman kan su za su shiga a dama da su wajen cimma wannan manufa.

Ma'aikatar ilimi ta kasar Sin ta kuma gabatar da wasu dokoki, wadanda za su inganta yanayin gudanar da makarantun na share fage, ciki hadda batun tsaron lafiyar dalibai, da na kare kamuwa da cututtuka, da kuma tsaron abinci.

Tsarin dai kashi na uku, ma'aikatar ilimi, da ta kudi, da sashen kula da ma'aikata, tare da kuma hukumar samar da ci gaba da gudanar da sauye sauye su ne suka gabatar da wannan sabon tsari kashi uku.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China