in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Palastinawa sun yi Allah wadai da shirin Isra'ila na gina matsugunansu a gabashin Kudus
2017-12-25 12:15:43 cri
A jiya Lahadi Palastinawa suka yi Allah wadai da shirin da Isra'ila ke yi na sake gina sabbin matsugunai kimanin 300,000 a gabashin birnin kudus.

Ma'aikatar harkokin wajen Palestinu ta bayyana cikin wata sanarwa cewa, shirin da Isra'ilan keyi tamkar mulkin mallaka ne da kuma cigaba da aikin mamaye matsugunan al'ummar Palastinu, kuma matakin da gwamnatin Isra'ilan ta dauka ta samu kwarin gwiwa ne daga yunkuri na baya bayan nan da shugaban Amurka Donald Trump ya yi na ayyana birnin kudus a matsayin babban birnin Isra'ila.

Kungiya mai fafutukar kwato 'yancin Palastinawa (PLO) ta yi gargadin cewa, akwai yiwuwar Isra'ilan zata yi wata babbar mamayar a kudus inda zata cigaba da fadada matsugunanta da kuma kwace ikon yankunan dake yamma da kogin Jordan.

A ranar 6 ga watan Disamba ne shugaban Amurka Donald Trump, ya ayyana birnin Kudus a matsayin babban birnin Isra'ila, kana ya umarci ofishin jakadancin Amurkar dake Isra'ila da ya koma birnin na Kudus wanda ake takaddama kansa, birnin wanda ya kunshi wuraren ibadu na mabiya addinin musulunci da na kirista da kuma na yahudawa.

Matakin na Trump ya haifar da zazzafar zanga zanga a daukacin kasashen larabawa dana musulmi a duk fadin duniya, kana lamarin ya haddasa tashin hankali tsakanin Palastinawa masu zanga zanga da dakarun Isra'ila a 'yan makonnin da suka gabata.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China