Mista Netanyahu ya yi furucin ne a wajen wani taron da majalisar ministocin kasar Isra'ila ke gudanarwa a ran nan, inda ya ce hukumar da MDD ta kafa don kula da 'yan gudun hijirar Palasdinawa, a hakika ita ce dalilin da ya sa aka dade ana fama da matsalar 'yan gudun hijirar Palasdinawa.
Ban da haka kuma, ya bukaci a mika ikon hukumar na kula da asusun tallafawa 'yan gudun hijirar Palasdinawa ga ofishin babban kwamishina mai kula da batun 'yan gudun hijira na MDD.
A ranar 2 ga watan da muke ciki ne, shugaban kasar Amurka Donald Trump ya rubuta a shafin sa na sada zumunta na Twitter cewa, zai dakatar da agajin da ake baiwa Palasdinu. A cewarsa, kasar Amurka ta kan baiwa Palasdinu dala fiye da miliyan 100 a ko wace shekara, amma duk da haka ba ta samu godiya ko kuma girmamawa daga bangaren Palasdinu ba, ganin yadda Palasdinu ta ki yin shawarwari tare da Isra'ila, game da yiwuwar kulla wata yarjejeniyar sulhu a tsakaninsu, in ji shugaban.(Bello Wang)