Mai magana da yawun rundunar sojan tsaron kasar Isra'ila ya ce, kungiyar Hamas ce ta tona wannan hanyar karkashin kasa, wadda ke kasan bututun jigilar iskar gas da man dizal wanda ya hada Isra'ila da yankin Gaza, kana tana karkashin wata tashar bincike ta rundunar sojan tsaron Isra'ila.
Rahotanni na cewa, sojojin Isra'ila sun dauki matakan soja na lalata wannan hanya ne a wani wuri mai suna Kerem Shalom dake kan iyakokin Isra'ila da Gaza.
A wannan rana, sojojin Isra'ila sun rufe yankin cinikayya na Kerem Shalom iyakarta da Gaza, wannan shi ne karo na biyu da sojojin Isra'ila suka rufe wannan muhimmin wurin cinikayya a cikin wata guda. A cewar rundunar sojan tsaron Isra'ila, kamata ya yi kungiyar Hamas ta dauki alhakin hakan.
Wannan hanya ita ce hanyar karkashin kasa ta uku ta Palesdinu da sojojin Isra'ila suka lalata a cikin watanni biyu.(Murtala Zhang)