Mataimakin babban darektan asusun na farko David Lipton shi ne ya bayyana hakan yayin da yake jawabi a bikin bude dandalin harkokin kudi na Asiya karo na 11 da ya gudana a yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin. Jami'in ya ce, nasarar da kasar Sin ta samu ya yi tasiri ga makomar tattalin arzikin duniya.
Lipton ya ce kasar Sin ita kadai tana samar da kaso daya bisa hudu na ci gaban tattalin arzikin duniya, kana ita ce kasar dake kan gaba a duniya a fannin cinikayya ta intanet, da fasahar mutum-mutumin inji da ma fasahar kere-kere.
Da ya juya ga batun gudummawar da kasar Sin take bayarwa a duniya kuwa, jami'in ya ce, kasar Sin tana bayyana ra'ayoyinta game da harkokin cinikayya da tattalin arziki, baya ga goyon bayan da take bayarwa ga ci gaban duniya baki daya.
Ya ce, babu tantama kasar Sin za ta ci gaba da bayar da gudummawa ga hukumomin kasa da kasa a shekaru masu zuwa. (Ibrahim Yaya)