Wasu rahotanni na nuna cewa, kusan al'ummar Najeriya miliyan 20 ke dauke da cutar hanta ko Hepatitis a turance, cutar da ake kamuwa da ita ta hanyoyin musayar jinni ko jima'i.
Da yake karin haske game da hakan, Mr. Wisdom Ihejieto na kungiyar likitocin kasar, ya ce a bana alkaluman yaduwar cutar sun dan yi kasa kadan, idan aka kwatanta da na shekarar bara, an kuma tattara su ne ta hanyar kididdigar bayanai da asibitocin kasar ke adanawa.
Ya ce, cikin wadanda ke fadawa hadarin kamuwa da cutar dai akwai jami'an lafiya, wadanda sanadiyyar amfani da allurai ko wukaken ayyukan kula da lafiya, kan kamu da ciwon ba tare da sun sani ba.
Cutar Hepatitis dai na kumbura hantar wanda ya kamu da ita. Kuma a cewar jami'in, karuwar yaduwar ta abu ne mai matukar tada hankali.
Mr. Ihejieto ya ce, za a shirya wani taron karawa juna sani a ranar 27 ga watan Mayu, domin tattauna hanyoyin fadakar da al'umma illar wannan cuta, da kuma dabarun kaucewa kamuwa da ita.(Saminu)