Soyinka, ya bayyana hakan a yayin zantawa da kamfanin dillancin labaran kasar Sin Xinhua a ranar Alhamis din nan a Abeokuta babban birnin jihar Ogun, ya ce aiwatar da wannan shirin tsakanin kasar Sin da Afrika zai yi matukar taimakawa fannin kiwon lafiya a fadin nahiyar ta Afrika.
Soyinka wanda tsohon jami'in hukumara lafiya ta duniya WHO ne, ya ce, tabbas wannan shirin zai taimakawa al'ummar nahiyar Afrika baki daya.
Ya kara da cewar wannan shirin zai yi matukar tasiri wajen musayar ilmi da fasaha a bangaren kiwon lafiya a nahiyar.
Sai dai jami'in ya kara da cewar, shirin zai fi amfani ne, idan ya kasance an gudanar da shi da zummar cin moriyar juna.(Ahmad Fagam)