in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hare-haren Boko Haram sun halaka mutane uku a Kamaru
2017-12-29 19:35:23 cri

Rahotanni daga Kamaru cewa, a kalla mutane uku ciki har da wasu 'yan kunar bakin wake biyu da wani farar hula ne suka gamu da ajalinsu, a wasu hare-hare biyu da ake zaton mayakan Boko Haram ne suka kaddamar a daren jiya Alhamis da kuma wayewar yau Jumma'a, a yankin arewa mai nisa na kasar ta Kamaru.

Harin na safiyar yau ya faru ne a Kordo dake yankin Kolofata dake kan iyakar Najeriya, inda 'yan kunar bakin wake biyu suka rasa rayukansu, sai dai babu wani farar hula da ya jikkata sanadiyar harin.

Shaidun gani da ido sun fadawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, 'yan kato da goro a yankin sun ga wasu mata biyu'yan kunar bakin wake kafin kaddamar da harin.

Bugu da kari, an kai wani hari a ranar Alhamis da dare a yankin Mayo-Moskota dake yankin arewa mai nisa na kasar ta Kamaru wanda ke kan iyaka da kasar Najeriya, lamarin da ya haddasa mutuwar farar hula daya.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China