in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 2 sun hallaka a harin Boko Haram a Kamaru
2017-12-12 11:11:48 cri
Wata majiya ta shedawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, a kalla fararen hula biyu ne suka mutu a sanadiyyar harin kunar bakin wake da mayakan Boko Haram suka kaddamar a yankin arewa mai nisa na jamhuriyar Kamaru a ranar Litinin.

Oumar, wani mazaunin yankin, ya bayyana cewa harin ya afku ne da misalin karfe 5:45 na safiya agogon yankin, bayan da wani matashi ya tada bomai boman dake jikinsa a cikin masallacin Abdoulaye dake Kerawa, a garin Mayo, inda harin ya hallaka limamin masallacin da ladanin.

Shima maharin ya mutu nan take.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China