Wata majiya ta hukumar tsaron kasar Kamaru ta sheda wa wakilin kwamfanin dillancin labaru na kasar Sin Xinhua cewa, mai yiwuwa ne harin na sanyin safiyar jiya, wasu ne da suka tsallaka cikin kasar ta Kamaru daga Najeriya suka kaddamar da shi. Sa'an nan ya ce an kwashe makaman sojojin da aka hallaka.
To sai akwai wadanda ke zargin cewa, mai yiwuwa 'yan a-ware da suke zaune a yankin masu magana da yaren Ingilishi ne suka kaddamar da harin.
A farkon watan da muke ciki, masu ra'ayin ballewar yankin dake magana da yaren Ingilishi daga kasar Kamaru, su hallakawa wasu 'yan sanda 4. Kafin hakan kuma, an samu barkewar zanga-zanga a yankin, inda a kalla masu zanga-zanga 10 suka rasa rayukan su, sakamakon arangama tsakaninsu da 'yan sanda.(Bello Wang)