in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Koriya ta Arewa ta yi allah wadai da taron ministocin harkokin wajen kasa da kasa kan batunta da Amurka ta kira
2018-01-19 13:18:03 cri
Jiya Alhamis ne, kakakin cibiyar nazarin harkokin kasar Amurka ta ma'aikatar harkokin waje ta kasar Koriya ta Arewa ya yi allah wadai da taron ministocin harkokin wajen kasa da kasa kan batun Koriya ta Arewa da kasar Amurka ta kira a birnin Vancouver na kasar Canada. Yana ganin cewa, a yayin da kasashen duniya suke nuna yabo kan yadda aka saussauta yanayin da ake ciki a zirin Koriya ta hanyar siyasa, da farfado da huldar diflomasiyya a tsakanin kasashen Koriya ta Arewa da Koriya ta Kudu, wannan taro da kasar Amurka ta kira game da Koriya ta Arewa a tsakanin kasashen da suka taba kai hari kasar domin a tattauna yadda za a matsa wa kasar Koriya ta Arewa lamba bai cancanta ba, kuma zai iya haddasa tashe-tashen hankula a zirin Koriya.

Haka kuma, ko da kasar Amurka ta nuna cewa, tana son yin shawarwari kan batun zirin Koriya, amma a zahiri, tana son rura wuta ne a yankin. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China