Shugaba Xi wanda ya bayyana hakan yayin zantawa ta wayar tarho da takwaransa na Koriya ta Kudu Moon Jea-in, ya ce kasar Sin tana goyon bayan yadda sassan biyu ke tattaunawa da yin musaya, matakin da sannu a hankali zai kai ga warware batun zirin Koriya.