A ranar Talatar da ta gabata ce, manyan jami'an kasashen biyu suka tattauna a kauyen na Panmonjum, ganawa ta farko tsakanin sassan biyu cikin kimanin shekaru biyu, inda kasar Koriya ta Arewa ta amince ta tura tawaga zuwa gasar wasannin Olympics da ma na ajin na kasassu da zai gudana a watan Fabrairu zuwa watan Maris a garin Pyeongchang dake gabashin Koriya ta kudu.
A lokacin tattaunawar da ke tafe, batun halartar gasar da Koriya ta arewan za ta yi zai kasance cikin ajendar ganawar, kamar yadda 'yan wasa da jami'ai daga DPRK za su tsallaka kan iyaka zuwa Pyeongchang, da yawan mutanen da za su halarci gasar da kuma wurin da za su zauna.