Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang wanda ya sanar da hakan Larabar nan yayin taron manema labarai da ya gudana a nan birnin Beijing ya ce, abin karfafa gwiwa ne yadda sassan biyu suka nuna kyakkyawan fata da rungumar juna a dai dai lokacin da yanayi a zirin Koriya ke kara tsananta.
Lu Kang ya ce, kasancewar kasar Sin wadda ke dab da zirin Koriya, ta yi maraba kana tana goyon bayan matakin da kasashen biyu suka dauka na kyautata alaka a tsakaninsu
Tattaunawa tsakani kasashen biyu wadda ita ce irinta ta farko cikin shekaru biyu, ta kai ga cimma yarjejeniya ciki har da yadda kasar Koriya ta arewa ta yarda ta tura tawaga zuwa gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu da za a gudanar a PyeongChang na kasar Koriya ta kudu da yin tattaunawar soja domin sassauta halin da ake ciki a zirin koriya.(Ibrahim)