in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tawagar masu aikin fasaha ta Koriya ta Arewa za ta kai ziyara Koriya ta Kudu
2018-01-16 12:26:06 cri
Jiya Litinin ne, wakilan kasashen Koriya ta Arewa da Koriya ta Kudu suka gana a dakin taron sasantawa na Panmunjom dake bangaren kasar Koriya ta Arewa, inda suka cimma matsaya game da ziyarar da tawagar masu fasaha ta kasar Koriya ta Arewa za ta kai kasar Koriya ta Kudu a lokacin gasar wasan motsa jiki ta Olympics na yanayin sanyi da kuma gasar wasannin Olympics ajin nakasassu da za a yi a birnin Pyeongchang na kasar Koriya ta Kudu.

A daren ranar 9 ga wata ne, Koriya ta Arewa da Koriya ta Kudu suka fidda wata sanarwar hadin gwiwa, bayan ganawar wakilan kasashen biyu a Panmunjom, inda suka bayyana cewa, bangarorin biyu sun cimma matsaya kan ziyarar tawagar masu fasaha ta kasar Koriya ta Arewa za ta kai kasar Koriya da Kudu da yin shawarwarin a tsakanin hukumomin sojoji na kasashen biyu da sauran batutuwa

Haka kuma, sun jaddada cewa, bangarorin biyu za su tattauna a fannoni daban daban, domin warware sabanin dake tsakaninsu ta hanyar yin shawarwari. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China