Ma'aikatar harkokin wajen kasar Sudan ta nuna gamsuwa da rahoton MDD, wanda ya nuna kyakkyawan tasirin da aka samu, daga shirin amshe makamai daga hannuwan fararen hula da ake yi a yankin Darfur, matakin da rahoton ya ce ya inganta tsaron yankin.
Sudan din ta kuma jaddada aniyar ta, ta ci gaba da hada kai da tawagar hadin gwiwar kungiyar AU da MDD, wadda ke aikin wanzar da zaman lafiya a Darfur ko UNAMID a takaice.
Ta kuma nanata muhimmancin hada karfi da karfe da sassan masu ruwa da tsaki wajen aikin wanzar da zaman lafiya, da samar da ci gaba, tare da aikin dawo da kyakkyawan yanayi a yankin na Darfur.(Saminu Alhassan)