in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
UNSC ya tsawaita wa'adin aikin tawagar wanzar da zaman lafiya a Darfur na kasar Sudan
2017-06-30 11:07:35 cri

A zamansa na ranar Alhamis, kwamitin tsaron MDD ya yanke shawarar tsawaita wa'adin aikin tagawar hadin gwiwar kiyaye zaman lafiya ta kungiyar tarayyar Afrika da MDD a yankin Darfur na kasar Sudan UNAMID, zuwa ranar 30 ga watan Yunin shekarar 2018.

Kwamitin tsaron MDD ya samun goyon bayan dukkan kuri'un da aka kada, kwamitin ya yi la'akari ne da halin tabarbarewar tsaro da yankin Darfur ke fama da shi, sakamakon yawaitar ayyukan kungiyoyi masu dauke da makamai a yankin, da matsalar bazuwar makamai a hannun jama'a, da sauran dalilai, don haka ya amince da tsawaita wa'adin tawagar wanzar da zaman lafiyar a yankin.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China