Omar Al-Bashir ya jadadda cewa, Gwamnati ba za ta lamunci tashin matsalolin tsaro a Dafur ba.
A jiya Laraba ne Shugaban ya gana da Gwamnan Dafur ta Arewa Abdulwahid Yousif, kuma yayin ganawar ne, Gwamnan ya shaidawa shugaban bukatar ci gaba da karbar makamai a matsayin matakin kawar da makamai baki daya daga yankin Dafur.
Shugaban kasar ya umarci Gwamnan ya ci gaba da tabbatar da tsaro da zaman lafiya da aka samu a yankin.
Har ila yau, Omar Al-Bashir ya umarci Gwamnan ya tsugunar da 'yan gudun hijira tare da maganace matsalolin tsaro da na jin kai.
A ranar 7 ga watan nan ne Gwamnatin Sudan ta kaddamar da gangamin karbar makamai a yankin Dafur. (Fa'iza Mustapha)