in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin kiyaye zaman lafiyar kasar Sin dake Darfur sun samu lambar yabo ta zaman lafiya ta MDD
2017-10-11 11:17:56 cri
Jiya ranar Talata, tawagar musamman ta MDD da AU dake Darfur wato UNAMID a takaice ta ba da lambar yabo ta zaman lafiya ga jami'ai da sojoji 225 na reshen sojojin kiyaye zaman lafiyar kasar Sin dake Darfur ta kasar Sudan.

Babban hafsan hafsoshin UNAMID ya halarci bikin, inda ya nuna yabo sosai ga ayyukan da sojojin kasar Sin suka yi. A cewar sa, kokarin da sojojin kasar Sun suka yi a fannin goyon bayan aikin raya kasa da na taimakon jin kai ya tantance samun yabo, sojojin sun kuma sada zumunci sosai tare da jama'ar Darfur. Don haka, UNAMID tana alfarma kan ayyukan da sojojin kasar Sin suka yi.

Tun bayan da suka soma aiki a watan Disamban shekarar da ta wuce, sojojin kiyaye zaman lafiyar kasar Sin sun kawar da wahalhalun da suke fuskanta a fannin yanayin halittu, tabarbarewar halin shiyyar, da yawan ayyuka a gabansu da dai sauransu, sun kuma samu nasarar kammala ayyukan kyautata gine-ginen filin jirgin sama, da na'urorin tsaro na sansanoni da dai sauransu, hakan suka samu yabo sosai daga wajen UNAMID da gwamnati da jama'ar wurin. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China