Wakilan al'ummomin yankin na Darfur, da gwamnatin Sudan, da wakilan MDD, da na kungiyar AU, da kuma na dakarun wanzar ta zaman lafiya na kungiyar tarayyar Afrika dake Darfur (UNAMID) sun shiga taron tattaunawar.
Da yake jawabi a lokacin bude taron, mataimakin shugaban kasar Sudan Hassabo Mohamed Abdul-Rahman, ya bayyana cewa, yankin Darfur yana samun kyautatuwa sakamakon yarjejeniyar da aka kulla ta birnin Doha game da zaman lafiyar yankin wato (DDPD) a takaice.
Ya nanata muhimmancin cigaba da tattaunawar da dukkan bangarorin da abin ya shafa domin kawo karshen tashin hankali a yankin.
Haka zalika, wakilin musamman na UNAMID, Jeremiah Mamabolo, ya bukaci kungoyoyin 'yan tawaye da ba su sanya hannu kan yarjejeniyar ba da su amince su shiga tattaunawar.(Ahmad Fagam)