in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An jibge rundunar jiragen sama masu saukar ungulu ta kasar Sin dake aikin wanzar da zaman lafiya a Darfur
2017-08-09 09:23:33 cri

Jiya Talata jiragen sama masu saukar ungulu guda 2 suka sauka a filin jirgin sama na Al Fashir da ke yankin Darfur a yammacin kasar Sudan, wadanda suke cikin rukuni na biyu na rundunar jiragen sama masu saukar ungulu ta farko ta kasar Sin. Haka ya nuna cewa an jibge dukkan jiragen sama masu saukar ungulu 4 dake cikin rundunar jiragen sama masu saukar ungulu ta kasar Sin ta farko a Darfur.

Sojojin kasar Sin masu aikin wanzar zaman lafiya za su yi aikin sintiri a sama, da leken asiri a fagen yaki, da yin jigilar mutane, da kuma kaiwa wadanda suka jikkata asibiti, kana da yin jigilar kaya da dai sauransu, bisa umurnin rundunar sojan musamman da MDD da kungiyar Tarayyar Afrika dake aiki a Darfur. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China