in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilan rundunonin sojin Koriya ta kudu da ta arewa za su tattauna da juna
2018-01-10 09:42:06 cri

Mahukuntan kasar Koriya ta kudu sun bayyana shirin da ake yi na zantawa tsakanin wakilan rundunar sojojinta da na makwafciyar ta Koriya ta arewa. Kaza lika Koriya ta arewa ta amince ta tura tawagarta zuwa Koriya ta kudu domin halartar gasar wasannin Olympics na lokacin hunturu, wadda za a gudanar nan gaba cikin wata mai zuwa a Koriya ta kudu.

A 'yan kwanakin baya ne dai wakilai biyar-biyar daga dakarun sojin kasashen biyu suka gana da juna, a wani mataki na wanzar da zaman lafiya, a taron da ya gabata a kauyen Panmunjom mai iyaka da kasashen biyu.

Bayan kammalar shawarwarin ne kuma aka fitar da sanarwar bayan taro, wadda ta ce Koriya ta arewa ta amince ta tura tawagarta zuwa gasar wasannin Olympcs da za a yi a Koriya ta kudu cin watan Fabarairu a birnin Pyeongchang, da kuma wasannin ajin nakasassu da zai biyo baya a watan Maris.

Kasashen biyu sun kuma amince da ci gaba da zantawa, tare da dakile rura wutar rikici, da wanzar da zaman lafiya a zirin Koriya, baya ga batun daukar matakan yafewa juna da hadin kai tsakanin sassan biyu.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China