'Rundunar 'yan sandan Kaduna ta ce, da misalin karfe bakwai na daren ranar Talata ne, wasu 'yan bindigan da ba'a san ko su wane ne ba suka yi wadannan mutane hudu kwanton bauna a kan hanyarsu daga Kaduna zuwa birnin Abuja, lamarin da ya kai ga kisan 'yan sanda biyu dake yi musu rakiya.
A halin yanzu 'yan sanda na kokarin kubutar da 'yan kasashen wajen da aka yi garkuwa da su.(Murtala Zhang)