Kwamishinan 'yan sandan jihar Zaki Ahmed, ya shaidawa manema labarai a birnin Fatakwal cewa, an kara baza jami'an tsaro a yankin na Omoku domin tabbatar da tsaro da kuma farautar wadanda ake zargi.
Da sanyin safiyar ranar Litinin ne aka kashe wasu mutane 16 tare da jikkata wasu 12, a lokacin da suka fito daga coci bayan gudanar da addu'o'in shiga sabuwar shekara.
Zaki Ahmed ya ce 'yan sanda za su tabbatar da kama mutanen, yana mai cewa sun shiga yankin ne ta koguna cikin kwale-kwale mai amfani da inji.
Kwamishinan wanda ya ce 'yan sandan ruwa na aikin sintiri a kogunan, ya roki mazauna yankin da su taimakawa jami'an da bayanan da za su taimaka wajen cafke wadanda ake zargin.
Ya kuma ba kamfanonin kasashen waje dake aiki a yankin shawarar komawa harkokinsu ba tare da wani tsoro ba. (Fa'iza Mustapha)