in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kara yawan taragon jiragen kasa a Najeriya
2018-01-05 09:27:41 cri

A jiya Alhamis ne shugaban tarayyar Najeriya Muhammadu Buhari, ya kaddamar da karin tarago 10 da kawunan jirage 2, cikin jerin jiragen kasa dake zirga zirga tsakanin biranen Abuja da Kaduna a arewacin kasar.

Hakan dai na zuwa ne yayin da mahukuntan Najeriyar ke kara kaimi, wajen kammala shimfida layukan dogo na zamani a yankin, aikin da gwamnatin kasar Sin ke tallafawa gudanar sa.

Yayin kwarya kwaryar bikin kaddamar da aiki da taragon a tashar Rigasa dake Kaduna, wadanda kamfanin gine gine na kasar Sin CCECC ya samar, shugaba Buhari ya ce burin gwamnatin sa shi ne bunkasa sha'anin sufurin jiragen kasa yadda ya kamata.

Ya ce layin dogo tsakanin Abuja zuwa Kaduna na cikin nasararorin sufuri da gwamnatin kasar ta cimma, duba da yadda aikin ke biyan bukatun al'ummar kasar. Kaza lika aikin na cikin matakan da gwamnati ke dauka, na farfado da fannin sufurin jiragen kasa da a baya ya durkushe.

Shugaba Buhari ya kara da cewa, gwamnatin sa ta kuduri aniyar hade dukkanin yankunan cinikayya da kasuwanci dake Najeriya da layukan dogo, a wani mataki na gaggauta bunkasar hada hadar tattalin arziki, da hade sassan kasar wuri guda.

An kaddamar da fara zirga zirga ta jiragen kasa tsakanin biranen biyu ne a ranar 28 ga watan Yulin shekarar 2016, domin samar da wata dama ta kyautata sufuri tsakanin Abuja da Kaduna, damar da ta bunkasa harkokin kwadago, da masana'antu da harkokin noma.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China