Ministan harkokin cikin gida na kasar Abdulrahman Dambazau, ya bayyana a Makurdi babban birnin jihar Benue cewa, Gwamnati ba za ta kyale mutane su rika daukar makamai suna kai hari kan al'ummomin da ba za su iya kare kawunansu ba, sannan kuma su tsere ba tare da an hukunta su ba, ya na mai jadadda cewa za a kara kokarin ganin an zakulo masu laifin.
Abdurrahman Dambazau ya bayyana wadanda suka aikata aikin na rashin imani a matsayin bata gari, ya na mai cewa za su fuskanci fushin hukuma.
Ya kuma yi wa iyalan da suka yi rashin 'yan uwansu yayin harin ta'aziyya
A ranar 1 ga wannan wata ne wasu 'yan bindiga da ake zargin makiyaya ne, suka kai farmaki kan al'ummomin yankunan Guma da Logo na Jihar Benue.
Haka zalika an samu rahoton wasu kashe-kashen a jihohin Kaduna da Kwara da Rivers a farkon shekarar nan. (Fa'iza Mustapha)