in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tattalin arzikin yawon shakatawa yana karuwa a duk duniya
2017-11-07 13:22:52 cri
Rahotanni daga taron harkokin yawon shakatawa na kasa da kasa wato WTM, wanda aka bude a jiya na cewa, kudaden da ake samu daga harkokin yawon shakatawa yana karuwa cikin sauri a dukkan fannoni, kuma adadin mutanen da suke zuwa yawon shakatawa yana karuwa a ko wace shekara, lamarin da ya samar da karin kudaden shiga ga wasu kasashen duniya.

A yayin taron, an gabatar da rahoto mai taken "yanayin bunkasuwar harkokin yawon shakatawa a duniya", inda aka bayyana cewa, a shekarar 2017 da muke ciki, yawan kudaden da aka samu ta fuskar yawon shakatawa ya kai dallar Amurka biliyan dubu 5.3, adadin da ya kai kashi 6.7 bisa dari na ma'aunin tattalin arziki na GDP. Wannan ya nuna cewa, a halin yanzu, harkokin yawon shakatawa na taka muhimmiyar rawa wajen raya tattalin arzikin duniya. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China